Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saukar Sarkin Kano Na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero A Filin Sauka Da Tashin Jiragen Sama Na Kano Ya Haifar Da Tankiya


Gwamna Kabir yayin da karbi
Gwamna Kabir yayin da karbi

Yanayi ya fara dumama a birnin Kano da kewaye sakamakon saukar mai martaba sarkin Kano da gwamnati ta cire Alhaji Aminu Ado Bayero a filin sauka da tashin jiragen sama na Kano.

Da nisalin karfe biyar na Asubahin Asabar din nan ne sarki ya sauka, inda ya gabatar da sallar Asuba bayan daya samu tarba daga dinbin magoya baya.

Hakan na faruwa ne sa'o'i kalilan bayan da shigar sabon sarkin Kano Muhammadu Sanusi cikin fadar Kano da tsakar daren jiya.

Yanzu haka dai Sarki Aminu na gida sarkin Kano na Nasarawa, tare dinbin magoya baya bisa rakiyar Jamian tsaro, yayin Sarki Sanusi ke gida Sarkin Kano na cikin gari.

A hannu guda kuma, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya baiwa kwamiahinan yan sanda na Kano umarnin kama sarkin Kano Aminu Ado Bayero bisa zargin sa da tada fitina a Kano.

Jamaar gari dai na cikin zulumi da yanayin rudani saboda tsaron abin da kaje ya zo.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da rahoto cikin sauti:

Jihar Kano Ta Fara Daukar Zafi Biyo Bayan Kafa Sabuwar Dokar Ta Rushe Sarauta Biyar A Jihar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:39 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG