Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Da Muhammadu Sanusi Kan Mukamin Sarkin Kano


Sarkin Kano, maimartaba Muhammadu Sanusi Lamido
Sarkin Kano, maimartaba Muhammadu Sanusi Lamido

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

"Bayan soke dokar masarautu ta jihar Kano ta 2019, hakan na nufin cewa masarautar Kano ta koma matsayinta gabanin dokar ta 2019", a cewarsa jim kadan bayan sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano.

Ya kara de cewa "hakan na nufin babu wani halastaccen sarki a Kano sai Sarki Muhammadu Sanusi".

Da safiyar yau Alhamis ne Majalisar ta yi wa dokar masarautun Kano ta shekarar 2019 garambawul, inda ta soke duka masarautun jihar biyar.

Wannan mataki ya biyo bayan sake nazari tare da zartar da dokar bayan da 'yan majalisar suka yi nasarar tsallake karatu na 2 da na 3.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Muhammad Bello Butu-Butu ne ya bayyana dalilan da suka janyo rushe masarautun.

Butu-Butu ya jaddada cewar soke dokar data rarraba masarautun Kano zuwa gida 5 zai taimaka wajen "dawo da martaba Kano data zube".

Ya kara da cewar, "raba masarautar Kano zuwa gida 5 ya rage kima da martabar jihar."

Da yake nanata wannan matsayi, Shugaban Masu Rinjaye a majalisar, Lawan Husseini Dala, ya bayyana illar rarraba masarautun ga al'adun Kano.

Husseini Dala yace, "masarautar ta kasance wata ma'ajiyar tarihi da al'adun Kano, wacce aka lalata sakamakon kirkirar karin masarautu.

Yayi karin hasken cewar, manufar gyaran dokar itace dawo da martaba da hadin kan da aka san masarautar Kano dasu.

Yayin ganawa da manema labarai, Husseini Dala ya bayyana cewar gyaran dokar baya nufin rushe masarautun 5.

Masarautun da aka rushe sun hada da na Kano da Bichi da Karaye da Gaya da Rano.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG