Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Kano: Muhammadu Sanusi II Ya Karbi Takardar Nadinsa


Sarkin Kano, maimartaba Muhammadu Sanusi Lamido
Sarkin Kano, maimartaba Muhammadu Sanusi Lamido

An mayar da Sanusi Muhammadu a matsayin Sarkin Kano bayan ya karbi takardar nadinsa daga Gwamna Abba Yusuf ranar Juma'a.

A yau ne Malam Muhammadu Sanusi II ya isa gidan gwamnatin Kano domin karbar takardar kama aiki a hukumance a matasayin sabon sarkin masarautar Kano daya tilo.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon Sarkin Kano bayan rushe masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira.

Wannan ya biyo bayan tsige basaraken a shekarar 2020 bisa yawan sabani da ake samu tsakanin gwamnatin Ganduje da Sarkin, wanda ake zargi da rashin biyayya da ladabi.

Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagoranci sallar Juma'a a masallacin gidan gwamnatin jihar, da ke kofar kudu.

Sarakunan gargajiya da sarakuna da sauran manyan baki ne suka halarci gidan gwamnatin yayin da aka baiwa Mai Martaba Sarki Sanusi takardar kama aiki.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG