Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Kabir Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Masarautun Kano


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu akan sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar ta yi wa kwaskwarima da ya rushe masarautu biyar a jihar.

Da safiyar yau Alhamis ne Majalisar ta yi wa dokar masarautun Kano ta shekarar 2019 garambawul, inda ta soke duka masarautun jihar biyar.

Gwamna Kabir Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Masarautun Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:45 0:00

Wannan mataki ya biyo bayan sake nazari tare da zartar da dokar bayan da 'yan majalisar suka yi nasarar tsallake karatu na 2 da na 3.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Muhammad Bello Butu-Butu ne ya bayyana dalilan da suka janyo rushe masarautun.

Butu-Butu ya jaddada cewar soke dokar data rarraba masarautun Kano zuwa gida 5 zai taimaka wajen "dawo da martaba Kano data zube".

Ya kara da cewar, "raba masarautar Kano zuwa gida 5 ya rage kima da martabar jihar."

Da yake nanata wannan matsayi, Shugaban Masu Rinjaye a majalisar, Lawan Husseini Dala, ya bayyana illar rarraba masarautun ga al'adun Kano.

Husseini Dala yace, "masarautar ta kasance wata ma'ajiyar tarihi da al'adun Kano, wacce aka lalata sakamakon kirkirar karin masarautu.

Yayi karin hasken cewar, manufar gyaran dokar itace dawo da martaba da hadin kan da aka san masarautar Kano dasu.

Yayin ganawa da manema labarai, Husseini Dala ya bayyana cewar gyaran dokar baya nufin rushe masarautun 5.

Masarautun da aka rushe sun hada da na Kano da Bichi da Karaye da Gaya da Rano.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG