Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautu Biyar A Jihar


Fadar Masauratar Kano
Fadar Masauratar Kano

Hakan ya biyo bayan wani mataki da Majalisar ta dauka a zaman da ta yi ranar Alhamis, 22 ga watan Mayun da muke ciki.

Majalisar dokoki ta jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta kirkiri sababbin masarautu a shekarar 2019.

Hakan ya biyo bayan wani mataki da Majalisar ta dauka yayin muhawara da aka tafka a zauren Majalisar a ranar Alhamis, 22 ga watan Mayun da muke ciki.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da Majalisar ta sake nazari tare da zartar da dokar bayan da suka yi nasarar tsallake karatu na 2 da na 3.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Muhammad Bello Butu-Butu ne ya bayyana dalilan da suka janyo rushe masarautun.

Butu-Butu ya jaddada cewar soke dokar data rarraba masarautun Kano zuwa gida 5 zai taimaka wajen "dawo da martaba Kano data zube".

Ya kara da cewar, "raba masarautar Kano zuwa gida 5 ya rage kima da martabar jihar."

Da yake nanata wannan matsayi, Shugaban Masu Rinjaye a majalisar, Lawan Husseini Dala, ya bayyana illar rarraba masarautun ga al'adun Kano.

Husseini Dala yace, "masarautar ta kasance wata ma'ajiyar tarihi da al'adun Kano, wacce aka lalata sakamakon kirkirar karin masarautu.

Yayi karin hasken cewar, manufar gyaran dokar itace dawo da martaba da hadin kan da aka san masarautar Kano dasu.

Yayin ganawa da manema labarai, Husseini Dala ya bayyana cewar gyaran dokar baya nufin rushe masarautun 5.

Masarautun da aka rushe sun hada da na Kano da Bichi da Karaye da Gaya da Rano.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG