Tun a safiyar yau ne sarki Sunusi Lamido ya samu rakiyar mataimakin gwamna da tawagar gwamnati zuwa masarautar Kano, bayan karbar takardar maida shi aiki a jiya Juma’a.
Sabon sarki Sunusi Lamido ya zauna a fada bayan da hakimai da masoya suka kawo masa mubaya’a.
A hannu guda kuma a safiyar yau din ne Sarki mai barin gado Aminu Ado Bayero ya iso filin jirgin saman Kano da jami’an tsaro ya kuma zarce gidan sarki na Nassarawa.
A wata ganawa da manema labarai mataimakin gwamna Injiniya Abdulsalam ya ce abubuwan mamaki na faruwa a safiyar yau kawo yanzu, inda ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara na musumman a harkokin tsaro suka rako tsohon sarki Kano.
Ya ce abune da ba’a taba yinsa ba a tarihin Kano, kuma hakan ka iya haifar da fitina da tada zaune tsaye.
A gidan Nassarawa kuwa shima sarki mai barin gado ya ce suna bin umarnin kotu ne kuma babu wanda ya fi karfin hukuma.
A halin da ake ciki dai tuni gwamnan Kano da mai martaba sarki Sunusi da manyan jami'an tsaro suka shiga wata tattauna ta sirri.
Dandalin Mu Tattauna