Ghana, Amurka Na Yunkurin Ganin An Mayar Da Mulkin Dimokradiyya A Nijar

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a fadarsa tare da mataimakiyar sakatarin harkokin wajen Amurka mai kula da sha'anin Afrika Molly Phee

Mataimakiyan sakatarin harkokin wajen Amurka mai kula da sha'anin Afrika Molly Phee ta bayyana cewa Ghana da Amurka za su ci gaba da hada hannu wajen tabbatar da mayar da dimokradiyya a Nijar.

ACCRA, GHANA - Daya daga cikin manyan jami’an diplomasiyyar Amurkar ta bayyana hakan ne bayan ganawarsu da shugaban Ghana Nana Addo a fadarsa da ke Accra babban birnin Ghana yayin wata ziyararta a wasu kasashen yammacin Afrika a baya nan.

Ghana na daya daga cikin jerin kasashen yankin yammacin Afrika da babbar jami'ar diflomasiyyar Amurka uwargida Molly Phee ta kai ziyara bayan Najeriya a kokarin da Amurka ke yi wajen lalubo hanyoyin maido da mulkin farar a kasar ta Nijar.

Sai dai bayan ganawarsu da shugaban Ghana Nana Addo, Molly Phee ta bukaci sojojin da suka kifar da Gwamnatin Bazaoum su kare martabar dImokaradiyya tare da sako Bazoum dama iyalinsa da ake tsare da su.

"Ghana da Amurka sun hada hannu wajen mayar da dImokradiyya a Nijar, kuma muna kira ga sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum da su kare martabar dImokradiyya a kasar tare da sako shi da iyalinsa" in ji ta.

Musah Shariff Nuhu Na Layya, tsohon jakadan Ghana a Guinea kana mai sharhi kan harkar demokradiyya ya ce ko shakka babu matakin da Amurka ta dauka na neman maido da mulkin farar hula ya dace.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a fadarsa tare da mataimakiyar sakatarin harkokin wajen Amurka mai kula da sha'anin Afrika Molly Phee

Amurka ita ce ja-gaba a fannin dimokradiyya a duniya in kuma ta tsaya wannan matsala ta dimokradiyya ta dore a yammacin Afirka to akwai matsala.

A baya-bayan nan sai dai ita kasar Amurka ta tisa keyar wasu zuwa gidan kaso bisa barazanar da suka yi wa dimokradiyyar kasar.

Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammaci Afrika ta ECOWAS tana ci gaba da lalubo hanyoyi domin ganin sojojin Nijar da suka hamabarar da gwamnatin Bazoum sun mayar da mulki ga farar hula.

Shugaban ECOWAS, Bola Ahmad Tinuba, ya fada a baya-bayan nan cewa kamata ya yi da sojojin da suka yi juyin mulki su yi koyi da mulkin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda bayan karɓe mulki ya dawo da dimokuradiyya a 1999 bayan shafe wata tara.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Your browser doesn’t support HTML5

Ghana, Amurka Na Yunkurin Ganin An Mayar Da Mulkin Dimokradiyya A Nijar. mp3