WASHINGTON, D.C - Shugaba Emmanuel Macron ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya yi wa jami'an diflomasiyya a ranar Litinin.
Macron ya kuma jaddada goyon bayansa ga hambararren Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum wanda ya jajirce akan cewa ba zai yi murabusa ba, abin da shugaban na Faransa ya kwatanta a matsayin jarumta.
A karshen makon da ya gabata wata tawagar malaman addinin Islama da ke kokarin sasanta rikicin ta sake isa Nijar domin warware wannan takkadama ba tare da karfin soja ba kamar yadda kungiyar ECOWAS ta yi gargadi akai idan sojojin juyin mulki suka ki maida kasar bisa tsarin dimokradiyya.
Har yanzu dai sojojin sun ki amincewa da duk wata hanyar sulhu inda suka ci gaba da tsara hanyoyin da za su ci gaba da rike madafun ikon kasar ta Nijar.
A kwanakin baya hukumomin sojin sun ce a ba su shekara uku kafin su mika mulki ga farar hula, bukatar da kungiyar ta ECOWAS ta yi watsi da shi.
Dandalin Mu Tattauna