Fashola Yayi Magana Akan Cibok

A woman carries a sign as she attends a protest demanding the release of abducted secondary school girls in the remote village of Chibok, in Lagos May 9, 2014.

​A lokacin da yake tarbar gungun masu gangamin neman gwamnati ta dauki kwararan matakai domin ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok, gwamnan Jihar Lagos Babatunde Fashola ya bayyana matsayinsa.
“Tunda mun saurari korafinku, kuma duniya ta saurareku, to nayi imanin cewa akwai wasu abubuwan da zamu iya yi, kuma wadannan abubuwan zasu iya zama yayata bayanai, da kuma samar da bayanan da zasu taimakawa masu neman wadannan dalibai, koda bayanan zasu taimaka ne wajen tabbatarwa ko watsi da shaidun da ake bukata,” a cewar gwamna Fashola.

Kasashen duniya kamar Amurka, da Britaniya, da Faransa, da Chana duk sunce zasu taimakawa Najeriya neman wadannan dalibai.

Kwararru daga Britaniya, wadanda suka kunshi jami’an diflomasiyya, dana agajin jin kai, dama jami’an Ma’aikatar Tsaro sun isa Najeriya Juma’ar nan domin baiwa gwamnatin Najeriya shawara akan yadda za’a samo wadannan yara.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace ya tabbata cewa daliban suna cikin kasar, ba’a ketara dasu zuwa Kamaru ba.