Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Mamalan Musulunci Sun Dauki Matsayi


Manyan malaman Musulunci kuma jami’an kungiyoyin ‘yancin bil adama na duniya sunyi Allah wadai da sace dalibai mata, suna kira haka a matsayin “sabanin addinin Musulunci”, kuma suna kira a sako daliban na Cibok.

“Wannan laifin da sauran manyan laifuka da wadannan ‘yan ta’adda suka dauka, sun saba manufar bayanannun koyarwar Qur’ani mai tsarki,” a cewar ‘Organisation of Islamic Cooperation (OIC) Figh Academy’ ko Makarantar Fiqihu ta Kungiyar Hadin kan Musulunci, a wata sanarwa.

A cikin makonnan, an kara sace yara mata sama da 10.

Kungiyar da ake cema Boko Haram tazo ne daga daya daga cikin yankuna mafi talauci a duniya, inda jarirai da dama suke mutuwa, da rashin ilimi, da matasa masu dunbin yawa marasa ilimi, wadanda ke saurin shiga harkokin ta’addanci. Masu fada a ji, sun sha kira akan gwamnatin Najeriya tayi wani abun talauci da rashin cigaban dake addabar arewacin Najeriya, lamarin da ya saba da kudancin kasar mai matsakaicin arziki, da kuma mafi yawan jama’a masu addinin Kirista.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG