Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayanna, an shafe sa’o’i ana gwabza fada tsakanin ‘yan bindiga da sojojin dake kan iyakar Jihohin Borno da Adamawa. A halin yanzu ba’a san adadin wadanda lamarin ya shafa ba.
“Mutane suna cikin barci, sai muka ji karar bindigogi irin wanda bamu taba jiba. Daman muna da sojoji wadanda basu fi su 15 ba. Mutanen suna da yawa gaskiya, sun kai motoci 15, haka suka kwana suna harbe-harbe, suna kone-konen abincin mutane” a cewar wani mazaunin garin wanda muka saye sunanshi.
Wani mazaunin garin shima yayi karin bayani akan irin barnar da ‘yan bindigan suka yi.
“Sun kwashe kayan abinci gaba daya, suka saka Bom, akwai gadar Adamawa da Borno sun saka Bom a wurin”, a cewar wani dan garin Liman Kara.
Da yake tabbatar da wannan hari, shugaban karamar Hukumar Madagali, Mr. Abawo yace kawo yanzu mutum dubu uku ne sukayi gudun hijira daga kauyen Liman Kara zuwa garin Madagali, yayinda da dama ke cikin mawuyacin halin rashin abinci.
Yanzu dai hankula sun koma ne akan rawar da jami’an kasashen waje zasu taka wajen yaki da masu tayar da kayar baya, wadanda har yanzu suke rike da daliban Cibok su kusan 300.