Trump, wanda ana iya cewa shine dan takarar da jam'iyyar Republican zata tsayar, ya fitarda wani fefen bidiyo jiya Litinin a dandalin Instagram, inda za'a ji ki'da mai tada hankali da sauti daga mata uku wadanda suke zargin tsohon shugaban kasar da cin zarafinsu a wajajen 1990.
Zuwa karshen bidiyon, sai ya nuna hoton tsohon shugaban na Amurka da matarsa zaune, yayinda wasu kalamai suka bayyana suna cewa, "dan zakara ya sake halinsa." Sai a ji muriyar Madam Clinton tana dariya.
A hira da aka yi da shi a baya bayan nan, Trump yace zai ci gaba da kawo wannan batu, domin ya tunasar da masu zabe irin rikicin da Mr. Clinton ya shiga a baya.
Akwai sabanin ra'ayi tsakanin masana siyasa, kan tasirin wannan mataki da Trump yake dauka.
Da yake maida martani kan wannan, wani kakakin kwamitin yakin neman zaben Madam Clinton, Brian Falon, ya gayawa tashar talabijn ta Bloomberg ranar Litinin cewa, caccakar da Trump yake yi, wata dabara ce ta kawar da hankalin masu zabe, daga yakin neman zaben da ya maida hankali kan bukatu da batutuwa daban daban da Amurka suka fi maida hankali a kansu.