Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump na jam'iyyar Republican ya caccaki abokan hamayyarsa


Donald Trump na jam'iyyar Republican
Donald Trump na jam'iyyar Republican

Biloniyan nan da ya shahara a harka gine-gine, sannan na sahun gaba a jam’iyyar Republican wato Donald Trump, ya caccaki kudurin abokan adawarsa guda biyu na ganin takararsa ta sha ruwa da cewa, wannan tsabar zakuwarsu ne na son mulki.

Abokan hamayyarsa Sanatan Texas Ted Cruz da gwamnan Ohio John Kasich, sun bayyana yunkurinsu a jiya Litinin na yadda suke kokarin nusar da jama’a garajen neman mulkin Trump, a matsayinsa na wanda bai taba rike wata kujerar siyasa ba.

Wanda suke ganin hakan wani mawuyacin abu ne ya sami tikitin zama dan takarar jam’iyyar ta Republican a wajen gangamin tsaida dan takara a watan Yuli mai zuwa, inda suke sa ran wakilan jam’iyya daga cikin su biyu ya kamata a zaba.

Inda Kasich yace zai tsayar da yakin neman zabensa na jihar Indiana da ke tsakiya maso yammacin Amurka, domin bawa Ted Cruz damar cin zaben dan takarar jihar a ranar 3 ga watan Mayu mai zuwa.

A yayin da shi kuma Ted zai dakatar da yunkurin yakin neman zaben cin jihohin Oregon da New Mexico da suke yammacin Amurka ranakun zaben jihohin ran 17 ga watan Mayu da kuma 7 ga watan Yuni, don bawa Kasich shima damar kada Trump a can.

Daga Ted har Kasich sun yarda da ci gaba da takarar kalubantar juna, a daya gefe kuma za su ci gaba da yakar Trump tare don dakile shi a wasu jihohin.

Trump ya aibata wannan yunkuri nasu da cewa, “Abin kunya ne a ce ‘yan takarar biyu da suka kawo karfi zasu hada kai wai don kawai su kada mutumin da kwata-kwata bai wuce watanni 10 da fara siyasa ba”.

XS
SM
MD
LG