Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba tare da bata lokaci zan canza manufofin harkokin wajen Amurka - Donald Trump


Donald Trump, hamshakin attajiri kuma dan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump, hamshakin attajiri kuma dan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican

Dan takarar nema shugabancin Amurka na sahun gaba a karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump, a jiya Laraba yace, ba tare da bata lokaci ba zai canza harkokin diflomasiyyar Amurka in ya ci zabe.

Ya sha alwashin fara la’akari da bukatar Amurka kafin komai, ya kuma bayyana harkokin diflomasiyyar Amurka a karkashin jagorancin Barack Obama a matsayin wata annoba.

Ya fadi haka ne a wani jawabin minti 38 a Washington Hotel, tare da kushe matakan Shugaba Obama game da diflomasiyyar Amurka.

Da ya koma kan abokiyar hamayyarsa kuma tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton sai yace bata da kwarewar zama shugabar Amurka.

Ya kuma yi alkawarin kawo karshen ISIS, sannan yace ba zai fadi yadda zai yi ba, amma su kam tasu ta kare in har ya zama shugaban Amurka.

A daya bangaren kuma abokin hamayyarsa na jam'iyyarsu dake biye da shi Ted Cruz, ya zabo tsohuwar shugabar kamfanin Kwamfuta na Hewlett Parkard wato Carly Fiorina, a matsayin mataimakiyarsa in ya zama Shugaban Kasa.

Carly ta taba takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Republican, daga baya ta janye a watan Fabrairun da ya wuce, ta kuma ce, ta yi matukar farin ciki da alfaharin wannan zabota da Ted ya yi.

Ted dai ya lashi takobin ganin ya dakile tasirin Donald Trump, don ganin jam’iyyarsu ba ta tsayar da shi a dan takararta ba a gangamin watan Yuli mai zuwa na jam'iyyar.

XS
SM
MD
LG