Dan Wasan Najeriya Victor Boniface Ya Yi Hatsarin Mota A Jamus

Victor Boniface (Bayer Leverkusen/Najeriya)

Wata majiya a kungiyar ta Leverkusen ta ce Boniface yana cikin koshin lafiya bayan aukuwar hatsarin.

Dan wasan gaba na kungiyar Bayer Leverkusen a gasra Bundesliga ta Jamus, Victor Boniface, ya yi hatsarin mota a ranar Lahadi.

Hatsari ya faru ne kwana guda bayan nasarar da kungiyarsa ta samu da ci 2-1 kan Eintracht Frankfurt.

Boniface, wanda ya zura kwallo ta biyu a minti na 72 a wasan ranar Asabar, a ranar Lahadi ya raba hotuna da bidiyo na motar da ta farfashe a shafukan sada zumunta na Instagram, kafin ya goge su.

Haka kuma, ya raba wani hoto da aka hango hannunsa da jini kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Wata majiya a kungiyar ta bayyana cewa Boniface yana cikin koshin lafiya bayan hadarin.

Jaridar Bild ta Jamus ta ruwaito cewa dan wasan wanda dan asalin Najeriya ne yana cikin motar a matsayin fasinja, a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Frankfurt, kuma ya sami rauni kadan a hannunsa kafin a kai shi asibiti.

Shafin yanar gizo na ‘yan sandan jihar Hessen ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne da safiyar Lahadi.