Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFCON 2025: Najeriya Ta Fitar Da Jerin ‘Yan Wasan Da Za Su Kara Da Benin, Rwanda


'Yan wasan Najeriya na Super Eagles
'Yan wasan Najeriya na Super Eagles

Fitar da sunayen ‘yan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada Bruno Labbadio a mstayin sabon kocin kungiyar ta Super Eagles.

Najeriya ta fitar da tawagar ‘yan wasan da za su kara a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi badi.

Shafin kungiyarta Super Eagles ne ya fitar da sunayen ‘yan wasa 23 a ranar Laraba.

Najeriya za ta kara da Benin a ranar 7 ga watan Satumba a birnin Uyo, sai kuma a ranar 10 ga watan Satumba ta dangana zuwa Kigali domin karawa da Rwanda.

Fitar da sunayen ‘yan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada Bruno Labbadio a matsayin sabon kocin kungiyar ta Super Eagles.

Wadannan wasanni za su zamanto zakaran gwajin dafi ga Labbadia wanda ya maye gurbin Finidi George.

Najeriya ce ta zo ta biyu a gasar AFCON da ta shude yayin da Ivory Coast da ta karbi bakuncin gasar ta lashe kofin bayan ta ci Najeriya ci 2-1.

Sau uku Najeriya na lashe kofin gasar ta AFCON, lokaci na na karshe shi ne a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu.

Ta kuma lashe kofin a shekarar 1994 a Tunisia sai kuma a shekarar 1980 inda ta karbi bakuncin gasar.

Ga jerin ‘yan wasan dna Super Eagles:

Masu tsaron raga: Stanley Nwabali, Maduka Okoye, Amas Obasogie.

Masu tsaron gida: William Troost-Ekong, Bright Osayi-Samuel, Olisa Ndah, Bruno Onyemaechi, Oluwasemilogo Ajayi, Calvin Bassey, Olaoluwa Aina.

‘Yan wasan tsakiya: Wilfred Ndidi, Raphael Onyedika, Alhassan Yusuf Abdullahi, Fisayo Dele-Bashiru, Frank Onyeka, Alex Iwobi.

‘Yan wasan gaba: Samuel Chukwueze, Victor Osimhen, Kelechi Iheanacho, Victor Boniface, Moses Simon, Ademola Lookman, Taiwo Awoniyi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG