Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Super Eagles Ta Dawo Najeriya Bayan Takaddamar Libya


Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)
Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)

Bayan nasarar da Najeriya ta samo a kan Libya a Juma’ar data gabata, an tsara cewa zasu sake karawa a birnin Benghazin Libya a gobe Talata, a ci gaba da gasar neman cin kofin nahiyar Afirka na 2025.

Tawagar kwallon kafar Najeriya Super Eagles ta dawo gida bayan takaddamar data sha a kasar Libya.

‘Yan wasan na Najeriya sun makale a kasar dake arewacin nahiyar Afirika tsawon fiye da sa’o’i 16.

Bayan nasarar da Najeriya ta samo a kan Libya a Juma’ar data gabata, an tsara cewa zasu sake karawa a birnin Benghazin Libya a gobe Talata, a ci gaba da gasar neman cin kofin nahiyar Afirka na 2025.

Gabanin karawar ne, tawagar Najeriya ta tashi zuwa Benghazi a wani jirgin shata, a jiya Lahadi.

Sai dai ‘yan wasan Najeriya suka sauka a filin saukar jiragen sama ta Abraq, wanda ake amfani da shi saboda jigilar aikin Hajji ne kawai.

Bayan da suka sauka ne, NFF ta tsara yin balaguro dasu ta mota zuwa wurin da za’a buga wasan sakamakon rashin ganin jami’an hukumar kwallon kafar kasar Libya.

Wata Sanarwa da sashen yada labaran NFF ta fitar a yau Litinin, tace an yi watsi da tawagar a filin saukar jiragen saman na Al-Buraq.

Haka shima bidiyon da bangaren yada labaran tawagar ta Super Eagles ya wallafa ya tabbatar da hakan, inda ya nuna ‘yan wasan da masu horas dasu da kayayyakinsu a yashe a filin saukar jiragen saman, sannan ma’aikatan tashar jiragen saman na nuna halin ko in kula da halin da suke ciki.

Da safiyar jiya Lahadi ne tawagar Super Eagles ta tashi zuwa Libya, gabanin karawar da zasu yi da takwararsu ta “Mediterranean Knights” a ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afrika a ranar ta 4.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG