Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce batun hana yaduwar fadan Isra’ila da Hamas, shi ne ya zamanto jigo a tattaunawar da suka yi da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da majalisar da kasar ta kafa a Tel Aviv don kula da sha’anin yaki.
Bayan tattaunawar, Blinken ya fadawa manema labarai matakan da ya zama dole a dauka domin ganin an kaucewa aukuwar irin harin da mayakan Hamas suka kai a ranar 7 ga watan Oktoba a kuma tabbatar da kyautatuwar makomar al’umomin Isra’ila da Falasdinu.
Kungiyar Hamas da Amurka ta ayyana a matsayin ta ‘yan ta’adda ta yi garkuwa da yahudawa 230 ta kuma halaka 1,400 a harin da ta kai.
Blinken ya kuma nanata goyon bayan Amurka ga Isra’ila na daukan matakan kare kanta, amma ya kuma ja hankalin hukumomin kasar da a kare fararen hula a yankin na Gaza.
“Akwai bukatar a kare rayukan Falasdinawa fararen hula, mun bayyana cewa, yayin da Isra’ila take kare kanta a yakin da take yi na kawar da mayakan Hamas, duba yadda ake tunkarar lamarin na da muhimmanci.” In ji Blinken.
Daruruwan dubban Falasdinawa ne suka rasa gidajensu sanadiyyar hare-haren saman da Isra’ila take kai wa kan Hamas a martanin harin da ta kai wa Isra’ilan.
Ma’aikatar lafiya a yankin gaza da hamas ke iko da shi ta fada a ranar alhamis cewa adadin mutanen da suka mutu ya haura dubu tara