Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Biden Ya Kai Ziyara Isra'ila


US President Joe Biden (L) speaks as Israel's Prime Minister Benjamin Netanyahu listens on prior to their meeting in Tel Aviv on October 18, 2023, amid the ongoing battles between Israel and the Palestinian group Hamas.
US President Joe Biden (L) speaks as Israel's Prime Minister Benjamin Netanyahu listens on prior to their meeting in Tel Aviv on October 18, 2023, amid the ongoing battles between Israel and the Palestinian group Hamas.

A Tel Aviv, shugaban Amurka Joe Biden ya dora alhakin fashewar da auku a Asibitin Gaza a kan dayan bangaren.

Shugaban Amurka Joe Biden ya je kasar Isra'ila ranar Laraba a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar zaman tankiya bayan wata gagarumar fashewa da ta auku a wani asibitin Gaza har daruruwan mutane suka mutu, lamarin da ya kuma janyo tsira wa juna yatsa tsakanin bangarorin biyu da ke fada da kuma haddasa zanga-zanga a fadin yankin.

Da yake nuna goyon baya ga dadaddar kasar kawancen Amurka, ga dukkan alama Biden ya goyi bayan Isra'ila, wadda ta musanta zargin ita ke da alhakin kai harin, ta kuma ce makamin roka da kungiyar mayakan Falasdinu ta harba ne ya taba asibitin.

Biden
Biden

"Na yi matukar bakin ciki da takaicin fashewar da ta auku a asibitin a Gaza a jiya, kuma bisa ga abin da na gani, ga dukkan alama dayan bangaren ne ya kai harin. Amma akwai mutane da yawa a waje da ba su da tabbacin hakan, a saboda haka akwai bukatar mu shawo kan abubuwa da yawa,” abin da Biden ya fada wa Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kenan a yayin da suka fara ganawa.

Nan take dai Fadar White House ba ta amsa tambayoyin da Muryar Amurka ta yi mata ba game abin da Biden ya ke nufi da ya ce “dayan bangaren,” kuma ko za su ba da hujja game da nazarin shugaban a kan maharan. A ranar Talata, kungiyar Jihadin ta musanta tana da hannu a fashewar.

Dama an shirya daga Tel Aviv Biden zai nufi birnin Amman domin ganawa da Sarki Abdallah na biyu na Jordan, da shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi na Masar, da kuma shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, domin tattauna yadda za a kai agajin jinkai ga al'ummar Gaza. Amma an soke zuwa taron kolin - da kuma kai ziyara Jordan bayan aukuwar fashewar.

ASIBITIN GAZA
ASIBITIN GAZA

Mayakan Hamas sun zargi Isra'ila da hannu a harin da aka kai a asibitin Ahli Arab da ke birnin Gaza, inda suka bayyana lamarin a matsayin "laifin kisan kare dangi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG