Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Amurkawan Da Suka Mutu A Harin Da Hamas Ta Kai Isra’ila Ya Kai 29


Shugaban Amurka Joe Biden (AFP)
Shugaban Amurka Joe Biden (AFP)

A ranar Juma’a Shugaba Joe Biden ya gana da iyalan Amurkawan da suka bata kana ya tattauna da iyalan wadanda Hamas take rike da su.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce akalla Amurkawa 29 ne aka tabbatar sun mutu a harin da Hamas ta kai Isra’ila a sama da mako guda da ya shude.

Wani Kakakin ma’aikatar ne ya tabbatar da adadin a ranar Asabar yana mai cewa har yanzu ba san inda wasu 15 suke ba da kuma wani mai izinin takardun zama a Amurka guda daya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana aiki “tukuru” domin neman inda suke.

A ranar Juma’a Shugaba Joe Biden ya gana da iyalan Amurkawan da suka bata kana ya tattauna da iyalan wadanda Hamas take rike da su.

“Suna cikin yanayi na alhini saboda ba su san inda ‘ya’yansu, mata da maza da yaransu suke ba.” Biden ya ce.

A ranar 7 ga watan Oktoba Hamas ta kai harin cikin Isra'ila wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Isra'ila ta mayar da martani kan yankin Gaza, lamarin da shi ma ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG