Ya zuwa yanzu dai dubban mutane ne suka mutu, kuma wasu da dama musamman Falasdinawa suka jikkata cikin kwanaki 8 da suka shude, sakamakon lugudan wuta da Isra’ila ke kaiwa yankin zirin Gaza, bayan wani harin kwantan bauna da mayakan Hamas suka kai a ranar Asabar ta makon jiya.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin siyasar kasa da kasa da kuma harkokin diflomasiyya a Jami’ar Bayero ta Kano, yace duk da salwanta rayukan bil’adama da kuma zub da jinin daruruwan mutane sakamakon hare haren, babu alamar yakin ka iya zuwa karshe a nan kusa.
“An sha zartar da kudurori a zauren majalisar dinkin duniya, musamman kan cewa Isra’ila kasa ce mai cin gashin kanta haka ita ma Falasdinu domin tabbatar da zaman lafiya a yankin, amma Isra’ila tayi burus da wadannan kudurori kuma duk lokacin da aka kai wannan batun zauren majalisar dinkin duniya babu wani mataki da ake dauka a kan Isra'ila.”
Tuni dai kungiyoyin Musulmi na duniya da masu kishin bil’adama suka fara Allah wadai da abin dake faruwa a zirin na Gaza. Zauren malaman addinin Musulinci na Najeriya wato Ulama Forum of Najeriya na cikin wadannan kungiyoyi.
Engr. Bashir Adamu Aliyu, sakataren Ulama Forum of Nigeria, ya ce babban abin kunya ne a ce majalisar dinkin duniya ta kasa samar da hanyar warware rikicin Falasdinu ta dindindin.
A daidai lokacin da kasashen duniya da yawa ke ci gaba da fuskantar kalubalen rikici dabam-dabam, Farfesa Sani Fagge ya ce abubuwan dake faru na da alaka da sabon tsarin bai daya da ake so a yi a duniya, wanda ke neman karfafa kasashen yammacin Turai a siyasar duniya da Talauta wasu kasashe, sannan kuma ga batun bazuwar makamai da wasu kungiyoyi da aka kirkira don cimma burin wasu kasashe.
Hakan dai na kara nuna bukatar dake akwai ga hukumomi, da gwamnatocin kashen duniya, da majalisar dinkin duniya, da sauran kungiyoyin rajin kare hakkin bil’adama su kara kaimi wajen daukar matakan da suka dace domin zaman lafiya da kwanciyar hankalin dan Adam a duniya.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna