WASHINGTON, D. C. -Sa'o'i bayan nan hukumomi sun bayyana sabbin bayanai game da shaidar da aka gano wajen tuhumar mai gidan da iyayen yaron ke haya da laifin daba wa yaron da mahaifiyarsa wuka.
Wadea Al-Fayoume, wanda kwanan nan ya yi bikin zagayowar ranar haihuwasa, ya rasu ne a ranar Asabar bayan da aka caccaka masa wuka da dama a wani mummunan harin da ya janyo Allah wadai daga ‘yan siyasa na yankin har daga jami'an fadar White House.
Hukumomi sun ce mai gidan da iyalın ke haya, Joseph Czuba, ya fusata game da yakin Isra'ila da Hamas, kuma ya kai musu hari bayan mahaifiyar yaron ta ba da shawarar su "yi addu'ar zaman lafiya."
A Bridgeview, wanda yanki ne mai yawan Falasdinawa, dangi da abokai sun tuna Wadea a matsayin yaro mai kirki da kuzari da son wasa.
An dauki gawarsa a cikin wani karamin farin Akwati gawa, wanda a wasu lokutan aka lullube da tutar Falasdinu.
Limamin Masallacin Mosque Foundation, Jamal Said, ya yi tunatarwa akan mutuwar yaron a lokacin jana’iza, amma kuma ya yi nuni da irin asarar rayuka da aka yi a yakin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da Hamas.
"Wadea yaro ne kuma ba shi kadai ba ne ake kai wa hari," in ji shi, ya kara da cewa "ana kashe yara da yawa a kasa mai tsarki, abin takaici, abin bakin ciki ne."
Da sanyin safiyar Litinin, Czuba ya gurfana a gaban kotu kan tuhumr kisan kai, yunkurin kisan kai da kuma laifukan nuna kiyayya.
Da yake karin haske game da tuhume-tuhumen da aka yi ranar Lahadi, ofishin Babban Jami’in dan sanda na Karamar Hukumar Will County ya bayyana cewa, “dukkan wadanda ake kai musu harin saboda ana zargin kasancewarsu Musulmi ne saboda rikicin Gabas ta Tsakiya da ya shafi Hamas da Isra’ilawa.”
Dandalin Mu Tattauna