Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Ya Sha Alwashin Murkushe Mayakan Hamas


Israel Politics
Israel Politics

Yayin da Isra'ila ke shirin kai gagarumin farmaki ta kasa a gaza, akalla Falasdinawa miliyan daya da suka rasa matsugunansu na fuskantar rikicin jinkai.

A yau Lahadi Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin kawar da kungiyar Hamas yayin da aka jibge sojojin Isra'ila 300,000 a kan iyakar zirin Gaza gabanin farmakin da suke shirin kaiwa ta kasa kan mayakan Hamas a yankin.

A karon farko shugaban na Isra'ila ya kira kwamitin majalisar ministocinsa na gaggawa, ciki har da dan majalisar dokoki daga bangaren adawa Benny Gantz, a wani abu da Netanyahu ya bayyana a matsayin na hadin kan kasa.

Da yake ganawa a shelkwatar sojan kasar dake Tel Aviv, Netanyahu ya ce dukkan shugabannin Isra'ila "suna aiki kai da fata, don cimma muradan kasar."

Israel Cabinet
Israel Cabinet

Ministocin sun tsaya shiru na 'yan mintoci don tunawa da Isra'ilawa 1,300 da aka kashe a harin da mayakan Hamas suka kai a ranar 7 ga watan Oktoba. Isra'ila kuma ta kaddamar da daruruwan hare-hare ta sama da makamai masu linzami kan Gaza tare da kashe Falasdinawa kusan 1,900.

Netanyahu ya ce "Hamas ta yi tunanin zata kawar da mu, amma mu ne za mu murkushe Hamas." Ya ce hadin kan da suka samu a siyasance “wani sako ne zuwa ga al’ummar kasar, makiya da kuma duniya baki daya.

Shugabannin na Isra’ila sun gana ne a daidai lokacin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai koma Isra’ila ranar Litinin don ci gaba da tattaunawa bayan ziyartar kasar a makon jiya. Babban jami'in diflomasiyyar na Amurka ya yada zango a kasashe bakwai a Gabas ta Tsakiya a cikin 'yan kwanakin nan, ciki har da Masar a ranar Lahadi, don aiki tare da kasashen larabawa abokan hulda don ganin an dakile yaki tsakanin Isra'ila da Hamas.

Israel Palestinians
Israel Palestinians

A ranar Lahadi jami'an gwamnatin Isra'ila sun ci gaba da yin kira ga mazauna yankin arewacin Gaza da su fice zuwa kudancin yankin, lamarin da ya janyo rudani a yankin sakamakon ayarin motoci da iyaye rike da ‘ya’yansu a hannu, suna tafiya da kunshin kayayyaki zuwa makoma mara tabbas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG