Bikin Ista: Paparoma Francis Ya Yi Wa Al'umar Ukraine Da Rasha Addu'a 

A jawabin sakon Ista da ya karfafa batun bege, ranar Lahadi Fafaroma Francis ya yi addu'o'i ga al'ummar Ukraine da Rasha, ya kuma yaba wa kasashen da suka karbi 'yan gudun hijira.

WASHINGTON, D.C - Paparoma Francis ya yi kuma kira ga Isra'ila da Falasdinawa da ke fuskantar mummunan tashin hankali a baya-bayan nan da su "mutunta juna tare da cimma hanyar sulhu."

Francis, tare da limaman cocin Katolika da yawa da dubban Kiristoci, sun yi taron sujada na rana mafi farin ciki ta mabiya addinin Kirista, inda aka kawata filin St. Peter's Basilica da furanni. Ranar Ista lokaci ne da Kiristoci suka yi imanin Yesu Krista ya tashi daga matattu bayan da aka gicciye shi.

Paparoma mai shekaru 86 a duniya, ya jagoranci bikin da jawabi da ya saba yi duk shekara game da wuraren da ke fama da rikici a duniya. Da yake ƙarfafa batun yarda da juna, tsakanin jama'a da kasashe," Francis yace farin cikin bikin Ista shi ne "yana haskaka duhun da lokuta da yawa, duniyarmu ke samun kanta a ciki."

Ana kiran saƙon na Ista na Paparoma "Urbi et Orbi" da harshen Latin, abinda ke nufin "zuwa ga birni da duniya."

-AP