Fadar Vatican ta ce Paparoma Francis, ya tsige wani tsohon babban limamin katolika a Amurka mai suna Theodore McCarrick saboda abin kunyar da ya yi.
A cikin watan Yulin bara, Francis ya amince da murabus din McCarrick da ya yi daga makarantar horar da malaman Katolika, biyo bayan zargin cewa ya aikata laifin lalata da yara kanana, da kuma manya a shekaru da dama a lokacin yana koyarwa.
Fadar Vatican ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar a cikin watan Janairun wannan shekarar cewa, ta samu McCarrick da aikata laifi, yayin da aka masa tambaya a wani mataki mafi tsarki da ‘yan darikar Katolika ke fadar laifukan da suka yi wa Ubangiji.
A wannan lokacin aka tabbatar da laifinsa na yin lalata da yara kanana da manya da kuma amfani da matsayinsa ta yadda bai dace ba.
“Doka ta shida ta ce karka aikata zina kuma wannan dokar na daya daga ciki dokoki goma na Littafi Mai Tsarki ko Bible da Allah ya saukar. Kuma wannan wani muhimmin umarni ne a addinin Yahudawa da na Kirista."
Facebook Forum