Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutane Sama Da 60,000 Ake Sa Ran Zasu Halarci Taron Jana’izar Paparoma Benedict


Makokin Paparoma Benedict
Makokin Paparoma Benedict

An tura tawagar wakilai daga gwamnatin Italiya da Jamus, wato kasar Paparoma Benedict ta asali.

Paparoma Francis ne zai jagoranci taron jana'izar tsohon Paparoma Benedict a dandalin St. Peter's ranar Alhamis. A ranar Asabar ne dai Paparoma Benedict ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

Sauran shugabanni da suka hada da sarki da sarauniyar Belgium, da sarauniyar Spain, da shugabannin kasashe kusan 13 za su halarci taron. Jakadun yawancin kasashe ne zasu wakilci kasashensu a fadar Vatican.

Tun a ranar Litinin aka ajiye gawar Paparoma Benedict a majami’ar St. Peter's Basilica, inda sama da mutane 160,000 suka je yi masa bankwana ya zuwa ranar Laraba da rana.

XS
SM
MD
LG