Miliyoyin mabiya addinin Kirista a fadin duniya na bikin Easter a yau Lahadi, wanda muhimmin lokaci ne da suke tunawa da tashin Yesu Almasihu bayan mutuwarsa.
A Fadar Vatican, an tsara Paparoma Francis zai gabatar da wani jawabin da ya saba yi a duk shekara ga mabiya adddinin na Kirista a duk fadin duniya, bayan ya kammala wani taro na sa-albarka.
A bara ne Paparoma Francis ya yi kira da a kawo karshen yakin Ukraine da ya kwatanta a matsayin “mara ma’ana” lokacin an fara yakin da wata biyu, sannan ya yi kuma yi kiran zaman lafiya a sauran sassan da ake fama da yake-yake a duniya, kamar Syria da Iraqi.
Paparoma, wanda bai gama murmurewa daga rashin lafiya ba, ya bi shawarar likitocinsa inda ya tsallake bikin ranar Juma’a wato ‘Good Friday Night’ wanda akan kwashe sa’a biyu ana yi.
A birnin Washington, Fadar gwamnatin White House na shirin gudanar da bikin nan da ake kira ‘Easter Egg Roll.’
Ana sa ran yara mutane kusan dubu 30, mafi aksari yara kanana, za su halarci bikin a ranar Litinin, wanda ya samo asali tun daga shekarar 1878.
A sassan duniya an dawo da bukuwa gadan-gadan, bayan da annobar coronavirus ta tilasata dakatar da su a shekarun baya.