Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirsimeti: Paparoma Ya Yi Fatan Samun Zaman Lafiya a Gabas Ta Tsakiya


Paparoma Francis a Fadar Vatican a lokacin da yake jawabin Kirsimeti
Paparoma Francis a Fadar Vatican a lokacin da yake jawabin Kirsimeti

Yayin da ake bukukuwan Kirsimeti a sassan duniya, shugaban darikar Katolika, Paparoma Farancis, ya ce fatansa a wannan shekarar shi ne nuna kauna a tsakanin jama’ar da suka fito daga sassan duniya.

Ya kuma yi fatan za a samu zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa da kuma rikicin Syria da na Yemen.

Shugagan darikar Katolika ya kara da cewa “Yesu Almasihu ya ce, “ceto na zuwa ne daga nuna kauna da mutunta dan Adam, da ya fito daga jinsuna da yarika da a’l’adu, amma kuma duk da haka dukkaninmu ‘yan uwan juna ne.”

Paparoma Francis ya kuma kara mayar da hankalinsa kan rikice-rikice da ke faruwa a Gabas Ta Tsakiya, inda ya yi fatan Isra’ial da Falasdinawa za su nuna kauna aa junansu ta hanyar sake hawa teburin tattaunawa, domin a samar da zaman lafiya da zai kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru 70 ana fama da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG