Shugabannin ma'aikatan kananan hukumomi sun nuna kin amincewarsu da cire masu wani kaso cikin albashinsu ko alawus.
Shugabannin sun zargi Alhaji Hudu Yusuf Ari babban sakataren ma'aikatar kananan hukummi da zama tushen rikicin. Suna cewa shi ne umalubaisan yukurin rage masu albashi da kuma rashin biyansu na har watanni uku. Wai Alhaji Ari ne ya shirya zabtare masu kudi.
Kwamred Shehu Isa shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin jihar yace sun zo ne su yi magan akan albashinsu. Yace sun samu bayanai cewa za'a zabtare wani bangaren albashinsu kana a biyasu sauran. Wai an cire wan bangare wanda ba za'a biya ba amma za'a biya sauran.
Yace sun tuntubi babban sakataren ma'aikatar dake kula da kananan hukumomi Alhaji Ari wanda ya tabbatar da hakan. Biyo bayan abun da babban sakataren ya tabbatar ma'aikatan sun zauna sun kuma yanke shawar kin karbar abun da za'a biyasu muddin bai cika ba. Su ba zasu karbi albashin ba muddin bai cika ba.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammad.
Your browser doesn’t support HTML5