Tawagar ta kai ta'aziya ne sabili da tashin bam a kasuwar Bauchi da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Tawagar a karkashin jagorancin ministan Abuja Sanata Bala Muhammad wanda shi ma dan jihar Bauchi ne ta kawo tallafi. Ta ziyarci kasuwar da aka kai hari da asibiti domin duba marasa lafiya da kuma sarkin Bauchi domin mika ta'aziya.
Sanata Bala Mihammad yace makasudin ziyarartasu ita ce su yi ta'aziya a madadin shugaban kasa da gwamnatin tarayya musamman ga 'yan kasuwa da harin bam din ya shafa. Yace sun kawo tallafi musamman ma 'yan kasuwa. Ministan ya kawo tallafin miliyan ashirin a madadin kansa da abokansa dake Abuja.
Muhammad Sani Sidi babban daraktan hukumar bada agaji ta kasa ta bayyana irin tallafin da gwamnatin tarayya ta tanada ma Bauchi da Gombe. Hukumar ta kawo magunguna daban daban da aka baiwa asibiti domin cigaba da kula da wadanda suka jikata. Shugaban kasa ya bada umurnin a taimaka masu da kayan gini. Duk irin abun da suka kai Bauchi shi ne zasu kai Gombe.
Gwamnan jihar Bauchi Malam Isah Yuguda ya bada umurnin a yi ginin dakin a kasuwar ta Bauchi. Ya bada siminti tirela biyar domin fara aikin. Shi ma dan takarar gwamna na PDP Muhammad Awal Jatau ya tara miliyan talatin domin tallafawa 'yan kasuwar.
A jihar Gombe gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwambo yayi alkawarin bada tallafi wa mutanen da bam din ya rutsa dasu a tashar motar Dukku yayin da ya kai ziyara. Shi ma shugaban PDP a jihar ta Gomben ya jajantawa wadanda abun ya rutsa dasu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.