Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Azare Sun Hallaka Wadanda Ake Zargi da Kai Hare-hare


Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda.
Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda.

Matasan garin Azare sun aika da wasu mutane biyu lahira da ake zargi su ne suka kai hare-hare a garin.

Wadanda aka kashe din sun hada da mace daya da namuji daya. Su ne ake zargin suna da hannu da tayar da bam a kasuwar Jigos inda ake hadahadar sayar da wayar salula jiya Lahadi.

An samu rahotanni dake karo da juna akan adadain mutanen da suka rasa rayukansu. Wani da yake aiki a asibitin gwamnatin tarayya ya tabbatar da mutuwar mutane 12 kana mutane fiye da 40 suka jikata.

Wasu mazauna garin kuma ganau sun kara bayani akan abun da ya faru. Sunce mutane 15 ne suka mutu. Mace ce ta tayar da bam din kamar karfe hudun yammacin Lahadi. Akwai wasu mutane da aka gansu tare da matar. Ita dai matar ta yi raga-raga.

Cikin mutanen da aka gansu da matar an kama biyu kuma nan take aka kashesu aka kuma konasu. Wani da ya hau babur yana gudu amma wai an kamashi.

Wannan harin na jiya shi ne na biyu cikin kwanaki tara. Jama'a sun ce suna fuskantar kalubale dangane da rashin tsaro a garin.

Kakakin hukmar yansandan jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed yace mutane 12 suka mutu kana 65 da suka jikata. Wasu da dama an yi masu magani aka kuma sallamesu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG