Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Nafada


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Rahotanni daga karamar hukumar Nafada, cikin Jihar Gombe na bayanin cewa ba’a jima ba, ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kaiwa garin hari, har suka kana ofishin ‘yan sanda, da makaranta, sannan sun kafa tutarsu a gidan sarkin garin.

Wani mutum wanda ya sha da kyar, kuma a lokacin da ya tattauna da Sashen Hausa, yana kan bishiya a boye yace “yanzu haka muna kan bishiya, sun zo sun watsa mu. Da nake magana, muna hango gidan Shaihin garin, sun zagaye gidan.”

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigan sun shiga garin ne da motoci, da babura sannan sun kona makarantu da Sakateriar garin.

‘Yan garin sun shaidawa Muryar Amurka cewa ‘yan bindigan sun kori sarki da fadawansa.

A kwanakin baya mayakan da suka ce su ‘yan boko haram ne sun kwace kauyuka da birane a jihohin Borno da Adamawa, dake arewa maso gabashin Najeriya lamarin da ya sa jama’a da yawa tserewa daga gidajensu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG