Gabanin sauyin gwamnati a matakin tarayya da akasarin jihohi Najeriya aranar jumaan makon nan wasu gwamnoni masu jiran gado na nuna alamun yin binciken abubuwan da basu gamsu dasu ba daga wadanda zasu gada.
Wannan ba zai rasa nasaba da labarum yadda wasu gwamnonin zasu bar jihohin nasu da jibgin bashi da wasu jihohin yakai naira miliyan dubu dari biyu.
Babu abinda yafi damun gwamnan jihar Bauci mai jiran gado a tutar APC Barister Iya Abubakar, inda yace maaikatan jihar na jin jikin rashin albashi.
‘’Idan kaje jihar Bauci kwanaki ukku bayan an karbo Kason jihar Bauci da gwamnatin tarayya ta shirya, watan da aka samu aka biya albashi kwana ukku bayan wannan lokacin idan kaje jihar idan wata matsalar miliyar 5 ta tashi ba za a iya yinta ba, duk wadannan makudan kudin da aka karba baya a jihar Bauci kusan babu abinda zaka iya nunawa na makuddan kudaden nan kuma duk da yake a baya nace ba zanyi bincike ba na irin wannan gwamnatin mai shudewa ba, amma kuma nayi alkawarin cewa dukkan kwabon jihar Bauci da aka yi almundahana akan sa ko ina ya shiga idan ALLAH ya yarda sai an karbo shi’’
Sai dai da aka ce masa jan layin da za a yi baishafi abubuwa da suka fito kan takardu wadanda suka nuna a zahiri gashi an nuna murdiya a wasu bangarori ba?
‘’Kwarai abin nufi ke nan muddin shaida ta nuna cewa anyi almundahana komai kankantar wannan dukiyar wannan bai shafi jan wannan layin ba dole a dawo wa jamaar jihar Bauci da dukiyar su’’
Anasa gefen gwamnan PDP na jihar Katsina mai barin gado Ibrahim Shehu Shema ya bugi kirjin cewa ba a bin gwamnatin sa ko sisin kwabo, kuma ma zai bar kusan naira biliyan hudu a asusun jihar don haka yace baya shakkar bincike.
‘’Kwanaki jamiyyar adawa ta buga a jarida tace a kananan hukumomin jihar Katsina duk basu da ko kwabo amma a zahiri karya ne domin yau gashi ina muku maganar cewa mun saki miliyan dubu takwasda dari biyar ga kananan hukumomin to daga sama suka fado kudin idan babu su cewa aka yi, cewa ma akayi wai na ciwo wa jihar Katsina bashi, wani ya taba zuwa gidan radio yace na ciwo wa jihar Katsina bashi na dala miliyan dubu sabain ko Najeriya bata ciwo bashin dala miliyan dubu sabain ba, amma aka tafi wannan gidan radiyon da wasu kafafen yada labarai aka ce na ciwo bashin dala miliyan dubu sabain, ni kuma na fada nace ban ciwo bashin ko sisin kwabo ba, idan mutum yace na ciwo bashi to ya buga ga jaroda mana cewa ga inda na ciwo shi, ga kudin da na ciwo ga kuma inda aka yi dasu, amma kawai sai azo a gaya wa mutane cewa an ciwo bashi ai ba ayi aiki ba to ko makaho dai ya shiga ihar Katsina ya shiga jihar katsina yasan anyi aiki.Ni abinda ma nake kira ga jamiyyun da suka shigo jihohi na Najeriya ko ba PDP ba
Ya kamata su tsaya su duba abinda kasar nan take ciki idan aka ce hayaniya za a tsaya yi shekara hudu kamar gobe ne ana nan ana hayaniyar sai kaga shekaran hudun saib ta kare’’
A yan kwanakin mika mulki tattalin arzikin Najeriya ya samu koma baya dan karancin man fetur da wutan lantarki da ya sanya bankuna rika rufewa da wuri yayin da kanfanonin sadarwa na aikawa da sakonnin halin oni yasu.