Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Wata Mata Kisan Gilla


Mata
Mata

A garin Bauci wata mata da ake kyautata cewa yar kunar bakin wake ne ta hadu da ajalin ta lokacin da gungun jamaa suka yi mata diran mikiya a sashin kasuwar yan gwari da ke kasuwar Muda Lawal a Bauci

Ga wanda akayi abin gaban idon sa da abinda yake shaidawa wakilin VOA

‘’Dazu ne aka samu wata mata da Bomb an kashe kuma anan Muda Lawal ne wajen kasuwar gwari anyi za a caje ta tazo zata shiga kasuwa tace bata yadda a caje ta ba akayi akayi tace ba za a caje ba aka matsa tace sam bata yadda ba saboda angan ta da kwalabe, a bayan ta dama jikin ta kuma ana tuhumar cewa abubuwan nan masu fashewa wato EXPLOSIVE DEVICE a turance, to kafin kace kwabo aka ci gaba da dukan ta wani soja ya kwace ta yasa a keke Napep amma kuma daga baya matasa suka hana suka fito da ita aka bubbugeta nan aka sa mata taya aka kona ta, yanzu haka yan sanda sun kewaye wurin gaba daya, kuma ance an baiwa DPO Na wurin umurni cewa a tattara gawar a tafi dashi yanzu dai mun bar Muda Lawal din amma yanzu dai abin ya dan lafa’’

Shima kakarin rundunar yan sandar na jihar Bauci DSP Haruna Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin

“Yau da musalin karfe bakwai na safe mun samu labarin cewa wata yarinya tazo zata shiga kasuwar Muda Lawal anzo za a caje ta domin aga menene a jikin ta dama suna yin wannan binciken amma sai ta ki ta bada kanta a caje ta sai taki dalilin haka sai mutane suka yi caa akanta suka sa mata taya suka kone ta, da muka samu labara kafin mu garzaya mu isa har ta kone, sai dai mun killace wurin sailin nan munje da mutanen mu masu warware abubuwan fashewa, yanzu mun kwantar da hankulla mun tabbatar da doka da oda a wannan wuri muna sintiri,’’

To da aka tambaye shi ko ina batun gawar nata? Sai yace 'Yan sanda sun dauka sun kai asibiti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG