A Bauchi dai wasu mutane sun jefi tawagar kemfen din shugaba Jonathan yayin da yaje yin gangamin neman zabe a garin.
Rahotanni sun nuna cewa abun da ya faru a Bauchin ya batawa shugaba Jonathan rai. To sai dai gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda ya daurawa 'yan siyasar jihar dake Abuja laifin abun da ya faru. Yayi zargin cewa su ne suka shirya makarkashiyar.
Idan ba'a manta ba ministan Abuja Sanata Bala Muhammad ya mayarda martani kan zargin na Yuguda. Yace jifa da aka yi masa ya batawa mutane rai sabili da haka don Allah su yi hakuri. Yace shi dansu ne shi kuma mai biyayya ne.
Sanata Bala yace mutane su san cewa Allah ne ya jarabcesu da mutumin da suka dauka cewa da ne amma basu san baragurbi ba ne. Sun dauka bafullatanin kirki ne ashe dan kwanta kwanta ne. Ya yi masu lif kamar mutumin kirki ashe ba sonsu ya keyi ba. Duk ladabin da suke yi ya zama abun banza. Ya kira su yiwa kansu kiyamar laini su san wane irin mutum ne Isa Yuguda yake.
Sanata ya cigaba da cewa a tunanensu na da ya kai ya rike kowane mukami ashe ko kansila ma bai kamata ya zama ba.
Amma kakakin kemfen din shugaba Jonathan Isa Tafida Mafindi yace a mayarda zuciya nesa. Yace su manyan arewa maso gabas basu yadda rigimar taci gaba ba. Yace suna ba gwamnan hakuri domin abun ya faru a jiharsa domin tsaron jihar yana hannunsa. Yace lokacin da suka kawo shugaban kasa yin gangami sun dankashi a hannunsa ba a hannun Sanata Bala Muhammad ba. Da a ce shugaban kasa yaje birnin tarayya yin gangamin zabe ne to da sai su barshi a hannun Sanata Bala Muhammad.
Mafindi yace idan irin wannan lamarin ya faru kada wani ya nemi hanyar buya yana kokarin turawa wani daban laifi. A yanzu Bauchi ke da shugaban jam'iyya. Sun san Muazu da Yuguda abokan juna ne. Idan akwai abun da ya bata masu rai su yafi juna. Yace Muazu, Yuguda da Bala su ne idon siyasar PDP a Bauchi. Sabili da haka babu dalilin da zai sa yara suyi jifa da masa da ruwan roba maimakon su zauna su ci.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka.