Batun Hijabi Muddin Zai Kawo Zaman Lafiya Abun a Amince ne

Hijab

Gamayyar kungiyoyin mata Musulmi da kuma masu kare hakkin mata sun gudanar da taron fadakarwa kan yadda ‘yan kunar bakin wake ke amfani da shigar mata Musulmi, domin aiwatar da aiyukan ta’addanci wanda ke shafawa mata Musulmi bakin jinni da kuma tsana a wasu sassa.

Manufar taron dai shine ankarar da hukumomin kasa kan kiraye kirayen da wasu kungiyoyin jama’a ke yiwa hukumomi na ganin an hana mata Musulmi, yin amfani da sitirar da addinin su ya umarcesu su yin amfani dashi.

Wata wace ta halarci taron Amina Abdullahi, tace “Gaskiya mu sanya Hijabi, muna gani shine sitiran mu, muna so a taimaka da naurorin bincike a kasuwani da makarantu da kuma wuraren taro.”

Shugaban dalibai Musulmi, na jihar Gombe, Malam Aminu Muhammad, yayi Karin haske kan yadda addinin Musulunci yayi batu kan sitirar mata Musulmi, Yana cewa “ Hijabi umarni ne na Allah da Manzon sa {S A W} akan mata, kuma adu’oi muke yi domin Allah ya kawo mana karshen wannan abun. Idan har aka ce matan mu sun fara yawo tsirara ta yaya zamu yi adu’a har Allah ya karba.

Shi kuwa Adamu Maidala cewa yayi duk wani matakin da hukuma ta dauka muddin zai kawo zaman lafiya abun a amince ne, saboda haka maganar wani Hijabi, fitar matan kansa idan ance hana su fita waje zai bamu zama lafiya, toh in an hana su fita yayi dai dai balle sa Hijabi.