Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwalliya ta Fara Biyan Kudin Sabulu Game da Matakan Wasu Gwamnoni Biyar


Shanun Fulani.
Shanun Fulani.

Bisa ga dukkan alamu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu game da matakin wasu Gwamnoni biyar da suka dauka na fatattakar barayin Shanu da suka addabi jihohinsu.

A kwanaki baya ne dai Gwamnoni jihohin Kaduna katsina Zamfara da kuma jihohin Kebbi da Nedja, suka kaddamar da shirin fatattakar wadannan barayin Shanu da suka yi sansani a dajin Kamuku dake cikin jihar Kaduna.

Kawo yanzu dai Fulani da ake yiwa satar shanu sun ce sun fara ganin a kasa Malam Muhammadu Shehu, mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Neja, yace “ mu dai yanzu sai godiyar Allah domin a baya a kullum mutane biyar zuwa shida zasu fito suna chigiyar Shanu, amma tunda aka dauki wannan mataki gaskiya fiye da wata daya yanzu babu wanda wa kawo chigiyar Shanu.”

Ya kara da kira ga Gwamnonin Kaduna, Neja, Zamfara da Kebbi da kada suyi sanyi a gwiwa domin makiyaya na farin ciki da wannan ci gaba da aka samu ya kuma bukaci Sarakunan Fulani da su bayyana duk wani bata gari ga kungiyar domin sanar da jami’an tsaro.

XS
SM
MD
LG