Bama-Bamai Biyu Sun Tashi A Damaturu Da Maiduguri

Sojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar Borno

Sai dai kuma hukumomi sun ce babu wanda ya rasa ransa a wadannan hare-haren da wani mai ikirarin shi kakakin Boko Haram ne yace su suka kai

Bama-bamai sun tashi a wasu birane biyu a arewacin Najeriya, kasa da mako guda a bayan da shugaban kasar ya ayyana kafa dokar-ta-baci a yankin.

Hukumomi sun ce babu wanda ya rasa rai a tashe-tashen bama-baman na daren laraba a biranen Maiduguri da Damaturu.

Wani mutumin da yace wai shi kakakin kungiyar nan ta Boko Haram ce, ya bayyana cewa sune suka kai harin. Yace hare-haren sune suka ayyana cikar wa'adin kwanaki uku da kungiyar ta ba 'yan kudancin Najeriya dake zaune a arewa da su tattara su koma yankinsu.

A wani lamarin dabam jiya laraba, wasu 'yan bindiga sun kashe mutane biyu a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

A ranar asabar shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ayyana kafa dokar-ta-baci a kananan hukumomi 15 na arewacin kasar, a bayan da aka yi watanni ana fuskantar mummunan tashin hankalin da hukumomin Najeriya suka ce 'yan kungiyar Boko Haram ke haddasawa.

Aika Sharhinka