Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Da 'Yan Boko Haram Sun Kara A Kano: Mutum 7 Sun Mutu


Wasu daga cikin wadan da ake zargin kungiyar Boko Haram da aka kama a Kano.
Wasu daga cikin wadan da ake zargin kungiyar Boko Haram da aka kama a Kano.

‘Yansanda a arewacin Najeriya sun bada labarin an kashe mutane bakwai a musayar wuta da mutane da ake zargin ‘yan kungiyar nan ne da ake kira Boko-Haram.

‘Yansanda a arewacin Najeriya sun bada labarin an kashe mutane bakwai a musayar wuta da mutane da ake zargin ‘yan kungiyar nan ne da ake kira Boko-Haram.

A yammacin jiya lahadi ne hukumomin kasar suka bada labarin cewa a ranar Asabar ce lamarin ya auku a kano, bayan da daya daga cikin mutanen ya ankara cewa jami’an tsaron sun sa ido kan gidansa, daga nan ne ya nemi doki kuma ‘yan kungiyar suka kai hari kan ‘yansanda. ‘Yan kungiyar ta Boko Haram hudu da ‘Yansanda uku ne suka halaka a musayar harbe harben.

‘Yansanda sun bada labarin sun dauki mataki kan ‘yan kungiyar Boko Haram a ‘yan kwanakin nan, suka kama mutane 14, suka kwace bindigogi da nakiyoyi daga wurare daban daban.
Ahalin yanzu kuma, ‘Yansanda a arewacin Kenya sun ce wata nakiya ta tashi ta halaka dansanda daya ta jikkata wasu biyu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Dadaab.

Hukumomi suka ce fashewar ta auku ne yau litinin yayin da jami’an tsaron suke cikin wata mota a cikin sansanin.

Saurari:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG