Limami wata coci a arewa maso gabashin Nigeria yace yan bindiga sun kutsa cocinsa ranar Alhamis da dare suna cikin ibada, suka kashe mutane shidda da raunana mutum goma.
Pastor Jonhson Jauro na cocin Deeeper Life a Gombe yace matarsa tana daga cikin wadanda aka kashe. Babu dai wata kungiyar data yi ikirarin kai harin, kuma har yanzu yan sanda basu ce uffan ba gameda harin.
A baya dai kungiyar Boko Haram tayi ikierarin kai wasu munanan hare hare akan Kiristoci, ciki harda wanda ta kai a ranar Kirisimeti akan wata cocin yan darikar Katolika a Madalla kusa da Abuja baban birnin taraiyar Nigeria, aka kashe fiye da mutane talatin.
Idan ba'a mance ba a makon jiya shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya ayyana dokar ta baci a yankuna goma sha biyar, ya kuma rufe kan iyakokin Nigeria da Niger da Chadi da kuma Kamaru. Shugaba Jonathan ya lashi takobin murkushe yan kungiyar Boko Haram. To amma masu cacar lamirinsa sunce bai tabuka wani abun kirki na tinkarar yan kungiyar ba.
Saurari