Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe akalla mutane 46 a Maiduguri da Damaturu

Mutane ne ke duba irin barnar da aka yiwa wani coci a Jajeri Maiduguri.
Mutane ne ke duba irin barnar da aka yiwa wani coci a Jajeri Maiduguri.

Hukumomi Nigeria sunce akalla mutane arba’in da shidda ne aka kashe a fafatwar da aka yi tsakanin jami’an tsaro da yan kungiyar Boko Haram.

Hukumomi Nigeria sunce akalla mutane arba’in da shidda ne aka kashe a fafatwar da aka yi tsakanin jami’an tsaro da yan kungiyar Boko Haram.

Wani mai magana da yawun soja yace tun ranar alhamis yan kungiyar Boko Haram suka fara fafatawa da jami’an tsaro a Maiduguri da Damaturu inda shedun gani da ido suka bada rahoto jin karajin harbe harbe da tashin bama bamai.

Wani magana da yawu kungiyar Boko Haram yace kungiyar kungiyar ta kaddamar da hare hare a biranen ne domin ramuwar gaiyar kashe yan kungiyar da jami’an tsaro suka yi a shekara ta dubu biyu da tara.

Cikin dai wadanda aka kasha harda jamian tsaro guda hudu wadanda bam din da aka boye a gefen hanya ya kashe su a Damaturu a ranar alhamis. Ana dai dorawa yan kungiyar Boko Haram hare haren da dama , Kungiyar tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai wasu hare hare ciki harda na ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abujan Nigeria.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG