Shugaba Goodluck Jonathan ya tattara manyan jami'an tsaronsa domin taron gaggawa da nufin tattauna tashin hankalin dake kara muni,w anda kuma ake dora laifinsa a kan 'yan kungiyar Boko Haram.
A wannan ganawa da aka yi jiya alhamis a Abuja, babban birnin kasar, shugaban ya bukaci manyan jami'an tsaro da su farauto mutanen dake kitsawa da daukar nauyin kungiyoyin tsagera, maimakon farauto wadanda suke bin umurnin da aka ba su kawai.
Wannan ganawa da shugaba Jonathan yayi da manyan jami'an tsaron ta biyo bayan hare-haren da aka kai cikin 'yan kwanakin nan a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ciki har da wadanda aka kai ranar kirsimeti har aka kashe mutane kimanin 40, akasarinsu mabiya addinin kirista.
A daren laraba, an ce wani abu ya fashe a garin Gombe dake arewacin kasar, amma babu rahoton da aka samu na jin rauni.
Ana dora laifin tashin hankalin a kan kungiyar Boko Haram wadda wasu da suke ikirarin magana da sunanta suka ce kungiyar tasu ce ta kai hare-haren bama-bamai da harbe-harbe a arewacin kasar da kuma Abuja babban birninta.
A ranar talata da maraice, wasu maharan da ba a san ko su wanene ba sun jefa bam hadin gida a cikin wata makarantar Islamiyya dake Jihar Delta a kudancin kasar, a wani harin da a bisa dukkan alamu na ramuwar gayya ce, har suka raunata yara 6 da wani balagaggen mutum guda daya.
Tashin hankalin yana kara fargabar cewa tsagera su na kokari ne su haddasa fada na addini a Najeriya. Ana ci gaba da wannan tashin hankalin duk da matakan da gwamnati ta ek dauka na murkushe kungiyar.
Masu hamayya da gwamnatin Najeriya sun soki lamirin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan a saboda ta kasa shawo kan wannan matsala ta Boko Haram.