Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 17 A Arewa Maso Gabashin Najeriya


'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya

An kai hare-hare na baya-bayan nan a Mubin Jihar Adamawa da kuma Gombe, babban birnin Jihar Gombe

Shaidu sun ce 'yan bindiga sun kashe mutane akalla 17 a arewa maso gabashin Najeriya, a hare-hare munana na baya-bayan a wannan yanki mai fama da fitina.

An kai hare-haren yau jumma'a a garin Mubi dake Jihar Adamawa, dab da bakin iyakar Najeriya da kasar Kamaru. Wani dan jarida a yankin ya fadawa Sashen Hausa cewa 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun bude wuta a wurare uku a garin.

Rahotanni daga yankin na fadin cewa an kai hare-haren ne a kan 'yan kabilar Igbo.

Wani mutumin dake ikirarin cewa shi ne kakakin kungiyar Boko Haram, ya fadawa 'yan jarida ta wayar tarho cewa sune suka kai wannan hari.

Wannan mutumin dake kiran kansa Abu Qaqa, ya kuma ce Boko Haram ce ta kai hari kan wata majami'a dake Gombe daren alhamis, har aka kashe mutane shida, aka raunata wasu goma.

A farkon makon nan kungiyar ta ja kunnen 'yan kudu dake zaune a yankin arewacin Najeriya da su fice daga yankin cikin kwanaki uku ko kuma a kashe su.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa ita ta kai wasu munanan hare-hare a 'yan kwanakin nan, ciki har da harin bam na ranar Kirsimeti da aka kai kan wata majami'a a kusa da Abuja aka kashe mutane fiye da talatin.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG