Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Boma-Bomai Sun Halaka Mutane 39 Ranar Kirsimeti


Ma'aikatan jiyya cikin motar daukan marasa lafiya su na kokarin ceton ran daya daga cikin wadanda harin boma-bomai ya rutsa da su a wata Majami'ar Katolika daf da Abuja a ranar Kirsimeti, 25 ga watan Disamba
Ma'aikatan jiyya cikin motar daukan marasa lafiya su na kokarin ceton ran daya daga cikin wadanda harin boma-bomai ya rutsa da su a wata Majami'ar Katolika daf da Abuja a ranar Kirsimeti, 25 ga watan Disamba

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin aikata wannan ta'asa

An zubar da jini a ranar Kirsimeti jiya lahadi a Najeriya inda bama-bamai akalla hudu suka kashe mutane 39, cikinsu har da wasu da dama a wata majami’ar darikar Katolika a kusa da Abuja, babban birnin kasar.

Kungiyar nan ta Boko Haram ta dauki alhakin kai wadannan hare-haren da a bisa dukkan alamu an shirya kaddamar da su sosai.

Harin bam mafi muni ya faru a kusa da Majami’ar Saint Teresa catholic dake garin Madalla, inda masu ibada suka taru suka yi addu’o’in Kirsimeti. Matasa da suka fusata da wannan zub ad jinin, sun kafa shingayen da suka cinna ma wuta a kusa da majami’ar, abinda ya sa har ‘yan sanda suka yi harbin iska.

Wani bam din ya tashi a kusa da wata majami’a a garin Jos, inda aka saba fuskantar fitina a tsakanin Musulmi da kirista. Jami’ai suka ce an bindige aka kashe wani dan sanda dake gadi a kusa da wurin daidai lokacin tashin wannan bam.

A Jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar, mazauna garin Gadaka sun ce wani bam ya tashi kusa da wata majami’a a lokacin da ake addu’o’in Kirsimeti. Ba a samu rahoton mutuwa ba. An kai hari na hudu a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe inda wani bam da aka boye a cikin mota ya kashe mutane uku a kusa da hedkwatar tsaron cikin gida ta Najeriya, SSS.

Shugabannin kasashen duniya sun yi tur da wannan tashin hankalin. Fadar White House ta bayyana shi a zaman ta’addanci na rashin kan gado, yayin da wani kakakin fadar Paparoma ta Vatican yace wadannan hare-haren matakan nuna tsananin kiyayya ne. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki-moon, yace babu wani dalili a doron duniya da za a iya amfani da shi domin kafa hujjar kai wadannan munanan hare-hare. Sakataren harkokin wajen Britaniya, William Hague, yace hare-haren bam aiki na ragwanci, yayin da ministan harkokin wajen Italiya, Guido Terzi yayi tur da hare-haren a zaman abin kyama.

Najeriya tana gwagwarmayar takalar wannan fitinar tashin hankali a arewacin najeriya, inda dakarun tsaron gwamnati suke fafatawa da ‘yan Boko Haram.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG