Babban Kwamandan Rundunar AFRICOM Ya Gana Da Shugaban Kasar Nijer Mohamed Bazoum

AFRICOM General Stephen J. Townsend

Babban kwamandan rundunar tsaro ta Amurka a nahiyar Afrika wato AFRICOM General Stephen J. Townsend ya yi rangadi a Jamhuriyar Nijer inda suka tantauna da shugaba Mohamed Bazoum game da batutuwan da suka shafi sha’anin tsaro da yaki da ta’addanci a kasar da ma yankin sahel baki daya.

Makasudun wannan ziyara ta General Stephen J. Townsend shine kara jaddada hukumomin Nijer goyon bayan Amurka a game da yakin da kasar ke kwafsawa da ‘yan ta’adda saboda haka bayan ganawa da babban kwamandan rundunar mayakan kasar ta Nijer General Salifou Modi kwamandan rundunar tsaro ta AFRICOM ya gana da shugaba Mohamed Bazoum inda suka tantauna akan batun tsaro.

Yace "mun tantauna akan yanayin tsaro a nan Nijer da ma yankin Sahel baki daya domin Nijer babbar kawa ce mai mahimmanci ga Amurka, mun yi Magana akan tallafin da ya kamata Amurka ta bai wa Nijer don murkushe ta’addanci, kuma na ji dadin yadda ra’ayoyinmu suka zo daya da na General modi da na Shugaba Mohamed Bazoum akan maganar yaki da ta’addanci."

Babban kwamandan na AFRICOM ya jaddada cewa Amurka za ta yi wa jami’an tsaron Nijer rakiya ta hanyar ba su kayan aiki da ba da horo da bayanan sirri domin karfafa masu guiwa a yaki da kungiyoyin ta’addanci.

Malama Aichatou Ambarka ita ce jami’ar hulda da manema labari a ofishin jakadancin Amurka a Nijer. Ta kuma ce za su cigaba ne da ba wa sojojinsu gudumuwa na kayan aiki, kuma su koya musu yanda ake yaki ba wai za su shiga yakin ba ne.

Tun a washegarin samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka ne kasar Amurka ta kulla huldar diflomasiya da jamhuriyar Nijer wace ta ta'alakka a karkashin tsarin da ake kira Approche 4D diflomasiya da aiyukan ci gaban jama’a wato developpement da dimkoradiya da batun tsaro wato defense.

Amurka na kan gaban kasashen dake tallafa wa Nijer a fannin tsaro sakamakon gamsuwa da yadda hukumomin kasar ke nuna alamun tsayin daka wajen neman hanyoyin samar da tsaro a yankin sahel.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti :

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Kwamandan Rundunar AFRICOM Ya Gana Da Shugaban Kasar Nijer Mohamed Bazoum