Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Afirka da Na Amurka Dake Taro Sun Kali Atisayin Sojojin Najeriya


 AFRICOM, hafsan hafsoshin Burkina Faso da Nijar a taron da su keyi a Abuja
AFRICOM, hafsan hafsoshin Burkina Faso da Nijar a taron da su keyi a Abuja

Sojojin Najeriya na musamman sun gudanar da wani atisayin nuna kwarewa da jajircewa musamman wajen ceto mutanen da ‘yan ta’adda suka sace, a wajen taron da sojojin Afirka dana Amurka suke yi a birnin Abuja.

Taron da hafshoshin sojojin kasashen Afirka da na Amurka ko AFRICOM suke ci gaba da yi a Abuja babban Birnin Taraiyar Najeriya, sun kalli atisayin gwada karfi da wata bataliyar sojan Najeriya ta musamman ta yi.

A atisayin sojojin Najeriya sun nunawa bakinsu yadda suke ceto mutanen da ‘yan ta’adda suka sace. Kazalika wasu jiragen sama na rundunar sojojin ruwan Najeriya din suka dinga ruwan bama bamai daga sama. Su ma sojojin kuntunbala sun yi ta harba bindigogin igwa sai da aka ceto wadanda aka sace.

Akan atisayin Mukaddashin babban hafsan tsaro na Amurka Janar Mark Veil ya ce abun da suka gani ya basu misalin irin kwarewa da jajircewar sojojin Najeriya. Injishi, idan suka ci gaba haka ko shakka babu zasu shawo matsalar tsarondake addabar kasar.

Shi ma babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai yace atisayin na nuna sabbin dabarun yaki da suka samu ne domin su iya shiga duk inda aka samu matsala, misali irin wuraren da Boko Haram suke boyewa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG