Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamandan 'Africom' Ya Fara Gudanar Da Ziyara A Nijar


Ziyarar Kwamandan 'Africom' A Nijar
Ziyarar Kwamandan 'Africom' A Nijar

Kwamandan Rundunar Sojan Amurka a Nahiyar Afurka, Janar Stephen Townsend, ya fara gudanar da ziyara a jiya laraba a jamhuryar Nijar, domin tattauna wasu mahimman batutuwa da hukumomin kasar musamman matsalolin ta’addancin da su ka addabi yankin Sahel.

A wunin farkon wannan ziyara ta kwanaki biyu, Janar Stephen Townsend, da ke samun danne gargada daga wasu mukarraban rundunar sojan Amurka a Nahiyar Afrika (wato Africom), ya gana da shugaban kasar Nijar, Issouhou Mahamadou, a fadarsa, inda su ka tattauna akan yakin da kasashen biyu ke gabzawa da kungiyoyin ta’addancin yankin sahel.

Janar Stephen na cewa mun yi tattaunawa mai armashi kuma a gaskiya kasar Amurka na farin ciki da samun Nijer a matsayi kawa.

"Shugaban ya sanar da ni cewa jinin sojan kasarsa da na Amurka ya zuba a lokaci guda a fagen fama. Ina ganin wannan wata kwakwarar hujja ce da ke nunin karfin huldar dake tsakanin kasashen nan biyu."

Yanayin da ake ciki a kasar Libya da halin da rundunar hadin gwiwar G5 sahel ke ciki, hade da batutuwan da su ka shafi tafiyar da aiki a rundunar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Mali (wato Minusma), da yanayin huldar kasar Amurka da jamhuriyar Nijar a fannin horon jami’an tsaro da bayar da tallafin kayan aiki, na daga cikin batutuwan da tawagogin kasashen biyu su ka tabo a yayin wannan ganawar, inji jakadan Amurka a Nijer Ambasada Eric P. Whitaker.

A ci gaban wannan rangadi, Janar Stephen Townsend, da tawagarsa za su ziyarci sansanin sojan saman Amurka na 1 da ke nan Nijar kafin daga bisani kwamandan na rundanar Africom ya isa a sansanin sojan Amurka na 2 domin tantance halin da dakarun ke gudanar da aikin tsaro.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da ke sahun gaban wadanda su ka hada gwiwa da kasar Amurka don murkushe kungiyoyin ta’addanci da su ka addabi yankin Sahel.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG