Ana gudanar da taron kwana biyu ne, da nufin karawa juna sani akan dubarun harhada bayanan sirri, a ci gaba da neman hanyoyin murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram da ISIS a yankin Tafkin Chadi.
Lura da mahimmancin bayanan sirri a yaki makamancin wanda kasashen na Tafkin Chadi ke kwabzawa, da kungiyoyin ta’addanci shekara da shekaru, ya sa cibiyar tsaro ta kasar Amurka a nafiyar Afirka, wato Africom shirya wannan taro.
Manufar taron ita ce a karawa juna sani akan dubarun samar da bayanan sirri a wannan lokaci da bayanai ke fayyace babbar alakar da ke tsakanin Boko Haram da kungiyar ISIS.
Mataimakin darekatan ofishin kula da horo a ma’aikatar tsaron Najeriya, Major Janar C.A Abraham, na daga cikin masu halartar wannan taro.
Ya kuma bayyana matsayin kara karfafa hadin kan da ke tsakanin kasashen Tafkin Chadi da Jamhuriyar Benin da kasashe aminai masu yaki da ta’addanci.
Taron wanda za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, a wani bangare zai kasance wata damar kara lakantar dubarun amfani da jiragen saman da kasar Amurka ta bai wa wadanan kasashe, a matsayin wata ingantattar hanyar hango abokan gaba in ji Janaral N’Gare Adoum shugaban ma’aikatar samar da bayanan sirrin sojan kasar Chadi.
Domin jin cikakken bayani, saurari rahoton da wakilinmu Souley Moumouni Barma ya aiko mana da Yamai.
Facebook Forum