Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na So Amurka Ta Mayar Da Rundunar Sojin AFRICOM Zuwa Afirka


Shugaba Buhari, yayin da suke taro da Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken (Twitter/@bashiraahmad)
Shugaba Buhari, yayin da suke taro da Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken (Twitter/@bashiraahmad)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nemi taimakon Amurka wajen yaki da kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi.

Cikin wata sanarwa da kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya rabawa manema labarai a ranar Talata, Shugaban na Najeriya ya ce, akwai bukatar Amurka ta sauyawa hedikwatar rundunar sojin wanzar da zaman lafiya a Afirka ta AFRICOM matsuguni.

A cewar Buhari, yin hakan, zai taimaka wajen kaucewa yaduwar matsalolin tsaro a yankin.

Yanzu haka hedikwatar AFRICOM na birnin Stuttgart na kasar Jamus.

Shugaban na Najeriya ya mika wannan kokon bara ne ga Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ranar Talata, yayin wani taro da suka ta yanar gizo.

Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka

Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa dagantakar Amurka da Najeriya da kuma yadda kasashen biyu za su fuskancin muradunsu.

“Kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya, babban abin damuwa ne, saboda abubuwan da ke faruwa a yankunan Sahel, tsakiya da yammacin Afirka da kuma yankin Tafkin Chadi.” Sanarwar Garba Shehu ta ce.

Buhari ya kara da cewa, Najeriya da jami’an tsaronta, sun himmatu wajen ganin sun shawo kan musabbabin wadannan matsaloli duk da irin girmansu.

Amma, “goyon bayan muhimman kawaye irinsu Amurka, abu ne da ba za a gaji da nanatawa ba, saboda sakamakon da rashin tsaro zai haifar, zai iya shafar dukkan kasashe.”

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram

“Hakan ya sa, ya zama abu mai muhimmanci, kasashe su hada karfi da karfe don a shawo kan wannan kalubale.”

Hakazalika yayin taron, Buhari ya yabawa kiran taron koli kan sauyin yanayi da Shugaban

Amurka Joe Biden ya yi a makon da ya gabata, yana mai cewa, hakan wata manuniya ce da ke bayyana amincewar Amurka ga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG