Wani sabon rikici ya kunno kai a tsakanin bangaren gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da kuma na tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar.
WASHINGTON, DC —
Wannan takaddama dai game da zaben shugabanin jam’iyar APC na jihar Adamawa ne, lamarin da ‘yan bangaren Atiku da kuma na ‘yan indifenda ke yin fatali da sunayen da gwamnan jihar ya bayyana cewa sune suka kamata su shugabanci jam’iyyar.
Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da yake ganawa da wakilan zasuyi zaben, wato “delegates” a turance, ya bayyana musu wanda yake so su zaba, batun da wasu suka ce baza ta sabu ba, bindiga a ruwa.
“A tabbata an zabi mutanenmu”, a cewar Admiral Murtala Nyako.
Amma Nyakon bai kammala wannan jawabi ba, wasu wakilai da ‘yan takara da suka hallarci taron sukayi fatali da wannan batu.
Abubakar Sa’idu Jambo, mai neman takarar shugaban matasa a jihar Adamawa bai goyi bayan Murtala Nyako ba.
“Ina Allah wadai da wannan bayani, bamu janye ba, kuma baza mu janye ba. Muna bukatan ayi demokradiyya”.
Yanzu dai an zura idanu a ga yadda wannan zabe na shuwagabannin jam’iyya zai kasance a jihar Adamawa larabannan, musamman ma a bangarorin jiga-jigen jam’iyyar.

Your browser doesn’t support HTML5